7 Yuni 2021 - 12:00
Mali : Za'a Rantsar Da Kanal Goïta, A Matsayin Shugaban Kasa

A Mali, yau Litini ne aka rantar da Kanal Assimi Goïta, a matsayin shugaban kasa, makwanni biyu bayan juyin mulki na biyu a kasar a cikin wata tara.

ABNA24 : Kanal Assimi Goïta, zai yi rantsuwar kama aiki ne gaban kotun tsarin mulki ta kasar.

Kafin hakan dai hankali ya karkata akan jawabin da zai gabatar bayan shan rantsuwar, musamman kan batun wa’adin da zai yin a rikon kwarya.

A sanarwar da ya bayar bayan kifar da mulkin tsohon shugaban rikon kwarya na kasar Bah N'daw, da firaministansa, kanal Assimi Goita, ya ce za’a gudanar da babban zabe a shekarar 2022, kamar yadda kasashen duniya da dama suka bukata ciki har da Faransa.

A kwanan baya dai Faransa, ta sanar da dakatar da haddin guiwa da take da sojojin kasar ta Mali.

342/